Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Manchester ta karbo Schweinsteiger

Bastian Schweinsteiger ya tabbatar da labarin zai bar kungiyar Bayern Munich zuwa Manchester United a jiya Lahadi idan har an kammala diba lafiyar shi.

Dan wasan Bayern Munich Bastian Schweinsteiger
Dan wasan Bayern Munich Bastian Schweinsteiger AFP/ODD ANDERSEN
Talla

A ranar Assabar ne Bayern Munich ta sanar cewa ta kammala yarjejeniya da Manchester game da Bastian Schweinsteiger kuma jaridun Birtaniya da Jamus sun ce Manchester ta biya kudi fam miliyan 14 akan dan wasan.

Schweinsteiger ya kulla yarjejeniyar shekaru uku ne da Manchester bayan ya shafe shekaru 17 a Bayern Munich.

Babu dai abin da Schweinsteiger bai lashe ba a Jamus, domin har da kofin duniya ya lashe wa kasar.

Ya yi haskawa 536 a Bayern Munich tun fara buga a kwallo a kungiyar yana dan shekara 18 a sherkarar 2002.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.