Isa ga babban shafi
Tennis

An kara yawan kudaden gasar US Open

An kara kudi a gasar US Open da kusan kashi 10 ga duk wadanda suka lashe kofin gasar a bangaren maza da mata. Duk wanda ya lashe kofin gasar zai karbi kudi dala Miliyan uku da dubu dari uku, kusan kashi 10 fiye da adadin kudaden da aka karba a bara.

Serena Williams ta lashe Roland Garros.
Serena Williams ta lashe Roland Garros. Foto: Reuters
Talla

Sannan ‘yan wasan da suka zo a matsayi na biyu za su kusan dala Miliyan biyu.
US Open dai za ta kasance gasa mafi tsokar kudi tsakanin manyan gasannin Tennis.

A makon jiya ne Serena Williams da Novak Djokovic suka lashe dala Miliyan biyu da Dubu Dari Tara a Wimbledon.

Wanda zai lashe Australian Open a bana zai karbi kudi dala Miliyan biyu da rabi, wadanda kuma suka lashe kofin Rolland Garros ta Faransa sun karbi kudi Dala miliyan biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.