Isa ga babban shafi
FIFA

FIFA za ta tsayar da ranar Zaben sabon shugaba

A yau Litinin ne kwamitin zartarwar hukumar FIFA zai gana a hedikwatar hukumar da ke kula da sha’ anin kwallon kafa duniya a birnin Zurich inda ake sa ran mambobin kwamitin za su tsayar da ranar da za a zabi wanda zai gaji Blatter.

Ofishin hukumar FIFA a Zurich
Ofishin hukumar FIFA a Zurich REUTERS/Ruben Sprich/Files
Talla

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da zargin cin hanci da rashawa ya bata sunan hukumar, inda duka kwanaki biyu ke nan da mataimakin Blatter Jeffrey Webb, ya musanta zargin ya karbi makudan kudade na cin hanci.

A daren jiya Litinin, rahotanni sun ce shugaban hukumar ta FIFA Seep Blatter ya gana da shugabannin kwallon kafa na nahiyoyin duniya kafin soma taron na yau.

Kuma wata majiya tace sun tattauna batun tsayar da ranar da ta dace a gudanar da zaben, ko da ya ke tsakanin Blatter da Issa Hayatou na Afrika da Sheikh Salman Bin Ibrahim Al Khalifa, na Asiya da Alfredo Hawit, da Juan Angel na kudancin Amurka babu wanda ya ce uffan kan tattaunawar.

Amma majiyoyi sun ce shugaban kwallon Turai Michel Platini, da ke adawa da Blatter ya ki amincewa da wasu bukatu a zauren tattaunarwar.

Planitini dai ana sa ran yana cikin wadanda za su yi takarar shugabancin hukumar FIFA, bayan Blatter ya bayyana yin murabus saboda zargin rashawa da ya dabaibaiye hukumar FIFA, lamarin da har ya kai aka cafke manyan jami’anta 14 gabanin sake zaben Blatter a ranar 29 ga watan Mayu.

Manyan kamfanonin da ke mu ‘amula da FIFA irinsu Coca Cola sun bukaci a gaggauta samar da sauyi a hukumar in ba haka ba za su katse huldarsu da ita.

Ana dai zargin jami’an FIFA da karbar biliyoyan daloli domin ba Qatar da Rasha damar karbar bakuncin gasar cin kofin duniya a 2018 da 2022.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.