Isa ga babban shafi
Wasanni

Guardiola ya mayar da martani ga Hitzfeld

Kocin Bayern Munich PEP Guardiola ya mayar da martani kan kalaman da tsohon kocin kungiyar Ottmar Hitzfeld ya yi kan kungiyar, inda ya ce , yan wasan dake Magana da harshen spaniyanci na neman mamaye kungiyar.

Pep Guardiola Kocin Bayern Munich
Pep Guardiola Kocin Bayern Munich Reuters / Michaela Rehle
Talla

A yanzu dai Bayern Munich nada yan wasa masu Magana da harshen spaniyanci guda 5 da ya hada da Xavi Alonso, Thiago alcantara, Javi Martinez da Juan Beret harma da Arturo Vidal, kuma daga cikin yan wasan kungiyar 29, 14 kacal ne yan kasar Jamus sai kuma David Alaba dan kasar Austria.

Tsohon kocin mai shekaru 66 ya ce dole ne Bayern Munich ta yi taka tsan tsan wajan daukan yan wasan kasashen ketere da yawa, kuma ta tabbatar cewa yaran Jamus ne aka fi amfani da shi a kungiyar.

Tuni dai Guardiola ya mayar masa da martani inda ya tunatar da shi cewa, a lokacin da shi kansa Hitzfeld ke rike da ragamar kungiyar, ai yan kasar Jamus kalilan ne cikin tawagar Bayern Munich da ta lashe kofin zakarun nahiyar Turai a shekara ta 2001.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.