Kotu ta goyi bayan hukuncin FIFA akan Platini
Kotun sauraren korafe korafen wasanni ta goyi bayan hukumar kwallon kafa ta duniya bisa matakin da ta dauka na dakatar da Michel Platini na tsawon watanni uku, lamarin da ya kara haifar masa da baraza game da samun shiga takakar shugabancin FIFA a shekara mai kamawa.
Wallafawa ranar:
A farko dai an yi zaton Platini wanda shi ne shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai kuma mataimakin shugaban FIFA , zai iya maye gurbin Sepp Blatter, wato shugaban FIFA, amma ya gamu da babban kalubale bayan an sanya shi cikin jerin jami’an FIFA da ake zargi da hannu a laifin cin hanci da rashawa.
A watan Octoban da ya gabata ne kwamitin da’a na FIFA ya dakatar da Platini da Sepp Blatter daga shiga harkokin wasannin kwallon kafa har na tsawon kwanaki 90.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu