Blatter ya bayyana a gaban kotu
Yau ne kotun hukumar kwallon kafa ta duniya ke fara shari’ar shugaban hukumar, Sepp Blatter da kuma Michel Platini, shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai bisa zargin su da aikata laifin cin hanci da rashawa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Blatter wanda ya isa kotun a Switzerland cikin bakar mota kirar Marsandi ya fadi cewa, zai kare kansa a gaban alkalan FIFA duk da jerin tambayoyin da ya ke fuskanta.
Kotun ta ajiye gobe Jumma'a domin sauraren Platini amma ya ce ba zai halarci kotun ba yayin da lauyansa zai je a madadinsa.
Hukumomin Switzerland na binciken Blatter sakamaon biyan kudaden da yawansu ya kai Swiss Franc miliyan biyu ba bisa ka’ida ba ga Platini a shekara ta 2011.
Amma dukkanin shugabannin biyu sun musanta aikata ba daidai ba.
Ana sa ran za a yanke hukunci na karshe nanda ranar litinin mai zuwa akan wannan badakalar a FIFA.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu