Isa ga babban shafi
FIFA

Blatter da Platini za su daukaka kara

Manyan jiga-jigan kwallon kafa da aka dakatar, Sepp Blatter da Michel Platini sun ce zasu kalubalanci hukuncin haramta ma su shiga sha’anin kwallo na tsawon shekaru 8.

FIFA ta dakatar da Sepp Blatter da Michel Platini na tsawon shekaru 8
FIFA ta dakatar da Sepp Blatter da Michel Platini na tsawon shekaru 8 Reuters
Talla

FIFA ta duaki matakin dakatar da shugabannin ne bayan kama Blatter da laifin amincewa da wasu kudade kimanin dala miliyan biyu zuwa ga Platini a 2011 ba tare da wata sheda ba a rubuce.

Ra’ayi dai ya banbanta tsakanin masu ruwa da tsaki ga harakar kwallon kafa musamman a Turai

Shugaban hukumar Holland Michael van Praag, kuma mataimakin shugaban hukumar kwallon Turai, yace hukucin da aka yanke akan Platini babban koma baya ne ga sha’anin kwallon kafa a Turai.

A cewarsa FifA na kokarin bin hanyoyin da zata wanke kanta daga badakalar rashawar da ta shafi shugabanninta.

Shugaban hukumar kwallon Ingila Greg Dyke yace babu yadda Blatter zai raba kan shi da rikicin FIFA.

Mista Dyke ya bayyana takaicinsa akan hukuncin da aka dauka akan Platini.

Tun tuni ne Dyke ya bayyana goyon bayan shi akan takatar Platini a matsayin shugaban FIFA. Amma yana ganin yanzu an gama da shi a harakar kwallon kafa.

Tsohon shugaban hukumar kwallon Turai Lennart Johansson yace hukuncin haramcin shekaru 8 akan Platini ya yi tsauri domin tamkar haramtawa ma shi shiga harakar kwallo ne na har abada.

Wannan dai shi ya kawo karshen kudirin Platini na shiga takarar zaben shugabancin FIFA da za a gudanar a watan Fabrairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.