Isa ga babban shafi
Wasanni

ESPN ya gayyaci 'yan takarar FIFA domin tafka muhawara

Gidan talabijin na ESPN na Amurka wanda ke watsa labaran wasanni ya gayyaci 'yan takarar shugabancin hukumar kwallon kafa ta duniya domin su zo su tafka muhawara game da makomar hukumar wadda badakalar cin hanci da rashawa ta dabaibaye. 

A rabar 26 ga watan Fabairu mai zuwa za a gudanar da zaben shugabancin FIFA.
A rabar 26 ga watan Fabairu mai zuwa za a gudanar da zaben shugabancin FIFA. REUTERS/Arnd Wiegmann
Talla

Mutane biyar ne dai ke neman wannan kujerar da suka hada da Jerome Champagne na Faransa da yarima Ali bin Hussain na Jordan da Gianni Infantino na Switzerland sai Tokyo Sexwale na Afrika ta kudu da kuma Sheik Salman na Bahrain.

A ranar 26 ne ga watan Fabairu mai zuwa za a gudanar da zaben na shugabancin FIFA yayin da aka dakatar da Sepp Blatter shugaban hukumar na tsawon shekaru 8 saboda zarginsa da hannu a badakalar ta cin hanci da rashawa.
 

Shi ma Platini, shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai, wanda a baya aka yi zaton zai gaji Blatter an dakatar da shi na shekaru 8 saboda zarginsa da karban kudade daga hannun Blatter ba bisa ka'ida ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.