Isa ga babban shafi
Ingila

Conte ne sabon kocin Chelsea

Kungiyar Chelsea ta ingila ta sanar da mai horar da ‘yan wasan kasar Italiya Antonio Conte a matsayin sabon kocinta a yau Litinin. Kungiyar ta sanar da cewa Conte ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekaru uku da za ta fara aiki idan an idar da gasar cin kofin nahiyar Turai a bana.

Antonio Conte sabon kocin Chelsea
Antonio Conte sabon kocin Chelsea REUTERS
Talla

Conte dai zai karbi aikin horar da ‘yan wasan Chelsea ne daga hannun Guus Hiddink da ke aikin rikon kwarya bayan raba gari da Jose Mourinho a watan Disemba.

Yanzu dai Conte ya kasance Dan Italiya na biyar da Chelsea ke dauka matsayin koci bayan Gianluca Vialli da Claudio Ranieri da Carlo Ancelotti da kuma Roberto di Matteo.

A 2014 ne dai Conte mai shekaru 46 ya karbi aikin horar da ‘yan wasan Italia kuma ya taimakawa kasar tsallakewa zuwa gasar cin kofin Turai da za a buga a Faransa bana.

Kafin nan kuma ya taimakawa Juventus lashe kofin Seri’a uku a jere da jere tsakanin 2012 zuwa 14.

Chelsea dai na matsayi na 10 ne a teburin Firimiya, kuma a bana za a kamala kaka Chelsea ba ta kofi ko guda sannan ba za ta shiga gasar zakarun Turai ba, wanda wannan babban kalubale ne ga sabon kocin kungiyar Antonio Conte.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.