Isa ga babban shafi
Wasanni

Tottenham ta rasa damar darewa saman teburin Premier

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta yi watsi da damarta ta darewa saman teburin gasar Premier ta Ingila bayan ta sha kashi a hannun West Ham a Upton Park a jiya Laraba.

'Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham
'Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham myfootballfacts.com
Talla

Da dai ta yi nasara, da kai tsaye ta zama ta daya a teburin gasar.

Amma har yanzu Leicester City ce ke jan ragama a da maki 57, sai Tottenham din da ke bi mata da maki 54 yayin da Arsenal ke a matsayi na uku da maki 51.

Manchester City mai matsayi na hudu, na da maki 47 yayin da ita ma Manchester United da ke matsayi na biyar da maki 47.

Manchester City dai ta gamu da babban kalubale dangane da fafutukarta ta neman daukan kofin premier na bana bayan Liverpool ta rama abinda ta yi mata a wasansu na karshe a gasar League Cup a ranar lahadin data gabata.

Yanzu haka dai dole ne Manchester City ta yi takan-tsantsan domin kungiyoyin da ke kasansa a teburi, za su iya kere ta.

Yayin da tuni Manchester United ta kamo ta a maki bayan ta doke Watford da ci daya mai ban haushi a jiya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.