Isa ga babban shafi
Wasanni

Infantino ya lashe zaben shugabancin FIFA

Gianni Infantino ya lashe zaben shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya bayan ya doke babban abokin takararsa a zagaye na biyu, Sheik Salman bin Ebrahim al-Khalifa.

Sabon shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Gianni Infantino
Sabon shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Gianni Infantino REUTERS/Arnd Wiegmann
Talla

Infantino ya samu kuri’u 115 a zagaye na biyu na zaben wanda aka gudanar a birnin Zurich na kasar Switzerland a yau juma'a yayin da Salman ya samu kuri’u 88.

Infantino mai shekaru 45 ya yi alkawarin jagorantar hukumar da sabon salo bayan ta gamu da badakalar cin hanci da rashawa wadda ta zubar da kimarta a idan duniya.

A zagayen farko, yarima Ali na Jordan ya samu kuri’u 27 yayin da Jerome Champagne ya tsira da guda bakwai kacal.

Tuni dai Tokyo Sexwale na Afrika ta kudu ya janye daga takarar tun kafin a fara kada kuri’u.

A bangare guda, kafin a fara, hukumar ta fitar da wasu sauye sauye, inda ta takaita wa’adin shugabancinta zuwa uku.

Sannan kuma wani sabon kwamitin zartarwa zai maye gurbin kwamitin zartarwa na yanzu, kuma zai kunshi mace guda daga kowace hukumar kwallon kafa ta nahiya.

Kasashe 207 ne suka kada kuri'ar a zaben na yau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.