Isa ga babban shafi
Wasanni

Leicester City ta lashe gasar Premier

Kungiyar kwallon kofa ta Leicester City ta lashe kofin gasar Premier ta Ingila bayan Tottenham da ke bi ma ta a teburi ta yi kunnen doki 2-2 da Chelsea a fafatawar da suka yi jiya Litinin a Stamford Bridge.

A karon farko kenan da Leicester City ta lashe kofin gasar Premier ta Ingila
A karon farko kenan da Leicester City ta lashe kofin gasar Premier ta Ingila Reuters
Talla

Da ma dai Tottenham ce ke baraza ga Leicester, amma ta gaza doke Chelsea a wasan na jiya, abinda ya saukake wa Leicester samun nasarar lashe kofin a karon farko tun bayan kafata shekaru 132 da suka gabata.

Wannan tarihin da kungiyar ta kafa ya sa miliyoyin jama’a daga sassan duniya gudanar da biki musamman a Ingila da Japan da Thailand.

Tuni dai kocin kungiyar Claudio Raneiri ya kira takwaransa na Chelsea Guss Hiddink ta wayar tarho, inda ya mika godiya ta musamman a gare shi saboda yadda 'yan wasansa suka rike Tottenham har suka tashi 2-2.

A karon farko kenan cikin shekaru 26 da Tottenham ta nemi doke Chelsea a Stamford Bridge amma hakarta ba ta cimma ruwa ba.

Tottenham din ce ta fara zura kwallaye biyu a mintina na 35 da kuma 44 amma daga bisani Chelsea ta farke a mintina na 58 da kuma 83, abinda ya zama babban koma baya ga Tottenham din.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Gianni Infantino ya bayyana wannan nasarar da Leicester City da samu a matsayin al’mara.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.