Brazil
Brazil ta nada Tite sabon koci
Brazil ta sallami kocinta Dunga tare da nada kocin kungiyar Corinthians Tite a matsayin sabon koci. Brazil ta kori Dunga ne bayan an yi waje da kasar a gasar Copa America tun a zagayen farko.
Wallafawa ranar:
Talla
Yanzu kuma babban kalubalen da ke gaban sabon kocin shi ne sauya abubuwa a kungiyar domin wasannin Olympics da za a gudanar a birnin Rio de Janeiro a watan Agusta.
Tite dai sananne a Brazil domin ya horar da kungiyoyi a kasar da suka da hada da Gremio da Atletico Mineiro da Palmeiras, kafin ya koma Corinthians inda ya lashe wa kungiyar kofunan lig biyu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu