Isa ga babban shafi
Wasanni

Del Bosque ya yi murabus daga horar da Spain

Mai horar da tawagar kwallon kafa ta Spain, Vicente del Bosque ya yi murabus daga aikinsa bayan da aka yi waje da kasar a gasar cin kofin kasashen Turai da ake gudanarwa a Faransa.

Kocin Spain mai murabus Vicent de Bosque
Kocin Spain mai murabus Vicent de Bosque REUTERS/Michael Dalder/File Photo
Talla

Kasar Italiya ce dai ta yi wa je da Spain mai rike da kambin gasar bayan ta doke ta 2-0

Kocin mai shekaru 65 ya lashe gasar cin kofin duniya da kuma gasar cin kofin Turai a tarihin kwallon kafar Spain.

Sannan kuma sau biyu yana lashe gasar zakarun Turai a lokacin da ya ke horar da Real Madrid.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.