Isa ga babban shafi
Wasanni

Ronaldo da Bale na cikin 'yan takarar gwarzon UEFA

Gwarzon dan wasan Portugal Christiano Ronaldo da abokinsa  a Real Madrid, Gareth Bale na kan gaba cikin sunayen zaratan ‘yan wasan kwallon kafa goma da za su fafata a takarar lashe kyautar gwarzon dan wasan UEFA na bana.

Christiano Ronaldo ya taimaka wa Portugal lashe kofin gasar kasashen Turai a Faransa
Christiano Ronaldo ya taimaka wa Portugal lashe kofin gasar kasashen Turai a Faransa REUTERS/Rafael Marchante
Talla

Ana ganin Ronaldo zai iya lashe kyautar saboda gasar zakarun nahiyar Turai da ta kasasahen Turai da ya lashe.

Kazalika akwai Antoine Griezmann na Faransa da ke taka leda a Athletico Madrid da aka sanya cikin jerin 'yan takarar.

Griezmann ya shiga jerin sunayen ne sakamakon rawan da ya taka a gasar cin kofin nahiyar Turai da aka kammala a Faransa, inda ya zura kwallaye 6.

Har wa yau akwai Messi na Barcelona da abokinsa Luis Suarez cikin sunayen wadanda za su fafata saboda laye kyautar.

A ranar 25 ga watan gobe ne za a sanar da dan wasan da ya lashe kyautar a Monaco bayan an fitar da jadawalin gasar cin kofin zakarun Turai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.