Isa ga babban shafi
Wasanni

Rasha ta kalubalanci hana ta shiga Paralympics

Kasar Rasha ta shigar da kara kotu domin kalubalantar hukuncin da kwamitin shirya wasan Paralympics na duniya IPC ya dauka na haramta mata shiga gasar masu bukata ta mussaman da za’ayi nan gaba kadan.  

Gasar Paralympics ta Lyon a Faransa
Gasar Paralympics ta Lyon a Faransa
Talla

Ma’aikatar wasannin kasar Rasha ta ce ba zata amince da a tauye mata hakkin shiga gasar paralympics din ba.

An dai dauki wannan matakin kan Rashan ne saboda zargin shan kwayoyin karin kuzari da aka yiwa ‘yan wasan Rashan tun gabannin fara wasannin Olympics a birnin Rio.

Sai dai kwamitin na Paralympics IPC ya ce dukkanin kwamitocin shirya gasar masu bukata ta mussamman na kasashen duniya sun amince da daukar wannan hukuncin kan Rasha.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.