An yi kuskuren kora na daga aiki- Allardyce
Tsohon kocin tawagar Ingila, Sam Allardyce da aka kora a jiya Talata, ya bayyana cewa, akwai kuskure a hukuncin da hukumar kwallon kafar kasar ta dauka a kansa.
Wallafawa ranar:
Hukumar ta sauke Allardyce ne bayan ya jagoranci kasar na tsawon kwanaki 67 sakamakon katobarar da ya yi a ganawarsa da jaridar Daily Telegraph, in da bayar da shawarwari kan karya dokokin cinikayyar ‘yan wasa.
Sannan kuma ya caccaki hukumar kwallon Ingila da kuma Roy Hodson da ya gada a matsayin kocin kasar.
Sai dai Mr. Allardyce ya shaida wa manema labarai a yau cewa, tarkon da ‘yan jaridu suka nada masa ya yi nasara kuma ya amince da haka.
'Yan jaridun dai sun gabatar da kansu ga Allardyce a matsayin 'yan kasuwa, in da suka tattauna da shi kan batutuwa da dama tare da nadan kalamansa cikin sirri, yayin da kocin ya shagala tare da furta kalaman da suka kai shi suka baro.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu