Isa ga babban shafi
Tennis

Murray ya lashe China Open

Andy Murray na Birtaniya ya lashe gasar China Open a jiya lahadi bayan ya doke Grigor Dimitrov a wasan karshe. Wannan ne kofi na 5 da ya lashe a bana kuma kofi 40 da dan wasan na Birtaniya da ya lashe a rayuwar shi.

Andy Murray na Birtaniya
Andy Murray na Birtaniya Reuters/Kevin Lamarque
Talla

Ana ganin Andy Murray zai karbe matsayin Novak Djokovic a matsayin zakaran Tennis a duniya.

Murray ya shiga sahun zaratan Tennis 16 da suka lashe kofuna 40, inda shiga jerin sahunsu Djokovic da Nadal da Roger Federer.

A bangaren mata Agneiszka Ranswanka ce ta lashe kofin na China Open bayan ta doke ‘yar wasan Birtaniya Johanna Konta
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.