Isa ga babban shafi
Wasanni

Sundowns ta lashe gasar zakarun Afrika

Kungiyar kwallon kafa ta Mamelodi Sundowns ta Afrika ta Kudu ta lashe gasar zakarun nahiyar Afrika a cikin wani yanayi mai kama da almara.

Mamelodi Sundowns ta Afrika ta Kudu
Mamelodi Sundowns ta Afrika ta Kudu Cafonline.com
Talla

Kungiyar ta samu nasara ne duk da cewa ita ce ta sha kashi a hannun Zamalek ta Masar da ci daya mai ban haushi a wasan karshe kuma zagaye na biyu da suka yi a jiya Lahadi a Alexandria na Masar.

To sai dai dama a wasan farko da suka yi a Pretoria, Sundowns ce ta lallasa Zamalek da ci 3-1, wannan ne yasa ta yi wa Zamalek fintinkau da yawan jumullar kwallaye kuma da haka ta lashe kofin.

Yanzu haka dai, Sundowns za ta halarci gasar kungiyoyin kwallon kafa na FIFA da za a gudanar a Japan a cikin watan Disamba mai zuwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.