Isa ga babban shafi
Wasanni

Messi zai jagoranci Argentina a fafatawarta da Brazil

Lionel Messi ya dawo da fara atasaye tare da tawagar kwallon kafar kasarsa Argentina, bayan rashin bugawa mata wasanni uku da yayi sakamakon raunin da ya samu.

Gwarzon 'yan wasan Duniya Lionel Messi
Gwarzon 'yan wasan Duniya Lionel Messi
Talla

Rashin bayyanar Messi a wasannin da Argentina ta buga na neman cancantar zuwa gasar cin Kofin Duniya na 2018, ya taimaka wajen rashin maki 7 da Argentina ta yi.

Yanzu haka Argentina na a matsayi na 5 cikin rukunin da ta ke, bayan rashin nasarar da tayi a hannun Paraguay da 1-0, sai kuma 2-2 da ta yi da kasashen Peru da Venezuela, a wasannin da Messi bai samu damar bugawa ba.

Mai horar da kasar Argentina Edgardo Bauza ya bayyana Messi a matsayin kaftin din kasar da zai joranci fafatawa da kasar Brazil a ranar 10 ga watan Nuwamba, sai kuma ranar 15 ga watan da zasu fafata da kasar Colombia.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.