Isa ga babban shafi

Sporting Lisbon ta lashe gasar Firimiyar kasar Portugal karo na 20

Kungiyar Kwallon kafa ta Sporting Lisbon, ta zama Zakaran gasar Firimiyar kwallon kafar kasar Portugal ta kakar wasannin 2023/24.

Sporting Lisbon Player
Sporting Lisbon Player © France 24
Talla

Rashin Nasarar da kungiyar Benfica ta yi Wacce ke Rufa Mata baya, a hannun tawagar Famalicao da ci 2-0 a jiya Lahadi, ya bawa kungiyar ta Sporting Lisbon, damar lashe gasar karo na 20 a tarihin ta.

'Yan wasan Sporting Lisbon na yin murna bayan lashe gasar Firimiyar kasar Portugal
'Yan wasan Sporting Lisbon na yin murna bayan lashe gasar Firimiyar kasar Portugal © ANTÓNIO PEDRO SANTOS/LUSA

Tawagar karkashin jagorancin mai horar wa Ruben Amorim, yanzu haka tana da maki 84 bayan buga wasanni 32, yayin da Benfica ke da maki 76, inda sauran wasanni biyu a kammala gasar.

Nasarar ta kungiyar ta bata damar wakiltar kasar ta Portugal a gasar Zakarun Nahiyar Turai UEFA Champions league na shekarar 2024/25, mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.