Isa ga babban shafi
Wasanni

Arsenal ta lalasa FC Basel da ci 2-0

Arsenal ta lalasa FC Basel da ci 2-0 a wasan zakarun turai, dan wasanta Walcott ne ya ci mata kwallayen, inda kwallon farko ya jefa shi minti 6 da soma wasa.

Theo Walcott ne ya zurawa Arsenal kwallaye biyu
Theo Walcott ne ya zurawa Arsenal kwallaye biyu Reuters / Darren Staples Livepic
Talla

Mai tsaron ragar Basel, Tomas Vaclik, ya yi kokarin hana kwallayen da Sanchez da Hector suka yi kokari zurawa ragarsu.

Ana su karawar Atletico Madrid ta yi wa Bayern Munich ci daya mai ban haushi. Wanda ke ba ta nasara ta biyu a wasanni da ta fafata a wannan kaka.

Franck Ribery da Robert Levandowski sun yi kokarin farkewa, amma bai samu ba. Kuma wannan shine karon farko da kocin Munich Carlo Ancelotti ya sha kaye tun soma tafiyar da kungiyar.

A sauran wasanni  na Zakarun Turai, PSG ta doke Ludogorets da ta karbi bakwancinta da ci 3-1.

Besiktas sun tashi kunan doki da Dynamo Kiev, yayin da Napoli ta cinye Benfica 4-2
sai FC Rostov da suka yi ci 2-2 da Eindhoven.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.