Isa ga babban shafi
Wasanni

Murray na yi wa Djokovic barazana

Dan wasan kwallon Tennis Andy Murray na ci gaba da neman jan raga a matsayin gwarzon dan wasan da ya fi kwarewa a kwallon Tennis a duniya.

Dan wasan kwallon Tennis Novak Djokovic
Dan wasan kwallon Tennis Novak Djokovic RFI/Pierre René-Worms
Talla

Wannan na zuwa ne bayan Murray ya doke  Jo-Wilfried na Faransa da ci 6-3 da kuma 7-6 a gasar Vienna Open, in da ya sake lashe wani kambin.

Yanzu haka dai Murray wanda ke a matsayi na biyu ya zama babban barazana ga Novak Djokovic mai matsayi na daya a fagen kwallon Tennis a duniya.

Nasararin da Murray ya samu a Beijing da Shanghai sun taimaka masa wajen naman doke Djokovic.

Matukar dai Murray ya samu nasara a wasan Paris Masters da za a yi a makon gobe, to lallai zai yi wa Djokovic fintinkau.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.