Isa ga babban shafi
FIFA

Kyautar Puskás: Kwallon da ta fi shahara a raga

Hukumar kwallon kafa ta FIFA ta fitar da jerin kwallaye 10 da aka jefa a raga daga sassan duniya da za a zabi ma fi shahara daga cikinsu. FIFA ta bude kofa ga masoya kwallon kafa daga 21 ga Nuwamba domin zaben kwallon da ta fi shahara a raga.

Kwallon da Neymar ya ci Villarreal da La Liga
Kwallon da Neymar ya ci Villarreal da La Liga youtube
Talla

Jerin ‘Yan wasa 10 da za a zabi kwallonsu mafi shahara a raga.

Kwallon Lionel Messi na Argentina da ya jefa a ragar Amurka a gasar Copa America a ranar 21 ga watan Yunin 2016. Dan wasan ya ci kwallon ne a firikik inda ya auna gwalkifa a lungu.

Kwallon Neymar na Brazil da ya ci Villarreal a gasar La liga. Dan wasan ya ci kwallon ne bayan ya janke dan wasan baya na Villarreal a sama sannan ya juya ya jefa kwallon a raga.

Kwallon Hlompho Kekana na Afrika ta kudu da ya jefa a ragar Kamaru a wasan neman shiga gasar cin kofin Afrika da kasashen biyu suka fafata a ranar 26 ga watan Maris na 2016. Dan wasan ya ci kwallon ne daga tsakiyar fili bayan mai ya lura mai tsaron gidan Kamaru ya fito.

Kwallon Simon Skrabb na Finland da ya jefa a raga kamar harbin kunama a ranar 31 ga watan Oktoban 2015 a gasar lig na Sweden.

Kwallon Mohd Faiz Subri na Malaysia da ya jefa a raga a ranar 16 ga watan Fabrairun 2016. Dan wasan ya ci kwallon ne a firikik inda kwallon da ya buga ta yi yamma ta dawo gabas ta fada raga.

Kwallon Mario Gaspar na Spain da ya jefa a ragar Ingila a wasan sada zumunci da kasashen biyu suka fafata a ranar 13 ga watan Nuwamban 2015. Dan wasan ya ci kwallon ne a raga tana zuwa daga sama.

Kwallon Marlone na Brazil dan wasan Corinthians da ya jefa ragar Cobresal a gasar Copa Libertadores.

Kwallon Saul Niguez na Spain da ya ci wa Atletico Madrid a karawarsu da Bayarn Munich a gasar zakarun Turai a ranar 8 ga watan Nuwamban 2015. Tun daga tsakiyar fili ya fara yanke ‘Yan wasan Bayern Munich ya kuma jefa kwallon a raga.

Kwallon Hal Robson-Kanu na Wales da ya jefa a ragar Belgium a gasar cin kofin Nahiyar Turai. Dan wasan ya yi wata juyawa ne ya ci kwallon a raga a ranar 1 ga watan Yulin 2016

Kwallon Daniuska Rodriguez ta Venezuela da ta jefa a ragar Colombia a gasar cin kofin duniya ta ‘yan kasa da shekaru 17 a ranar 14 ga watan Maris na 2016.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.