Kungiyar Real Madrid ta kafa sabon tarihi
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid sake kafa sabon tarihi na buga wasanni da dama ba tare da samun rashin nasara ba.
Wallafawa ranar:
Nasarar da kungiyar ta samu kan Deportivo la Coruna da kwallaye 3-2 a wasan da suka buga jiya na gasar Laliga, ya bawa kungiyar damar kafa tarihin buga wasanni 35 ba tare da anyi nasara a kanta ba karkashin sabon mai horar da ita Zinadine Zidane.
Wannan tarihi dai ya zarta wanda kungiyar ta taba kafawa a shekarun 1988 da kuma 1989 karkashin mai horar da ita Leo Beenhakker, inda kungiyar ta fafata wasanni 34 ba tare da an samu nasara a kanta ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu