Isa ga babban shafi
Wasanni

Mourinho na maraba da karin kasashe a gasar cin kofin Duniya

Mai horar da kungiyar Manchester United Jose Mounrinho ya bayyana goyon bayansa kan bukatar shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino, na kara yawan kasashen da zasu rika halartar gasar cin kofin kwallon kafa na duniya.

Mai horar da kungiyar Manchester United Jose Mourinho
Mai horar da kungiyar Manchester United Jose Mourinho REUTERS/John Sibley/Fil
Talla

A cewar Mourinho, kara yawan kasashen zai taimakawa kasashen da basu da karfi a harkokin kwallon kafa samun kwarin gwiwar yin hakan.

Zalika mai horar da kungiyar ta Manchester United, ya ce Karin zai taimaka wajen yiwa kasashen duniya kaimi game da inganta harkokin wasanni, musamman ma fagen kwallon kafa.

A cikin shekarar da ta gabata ne shugaban FIFA Infantino ya gabatarwa da majalisar zartarwar hukumar bukatar neman kara yawan kasashen da zasu rika halartar gasar cin kofin duniya daga 32 zuwa 48 daga shekara ta 2026.

Sai dai kuma wasu daga cikin hukumomin kula da kwallon kafa na nahiyar turai sun bayyana shakku game da sabon tsarin.

A dai cikin wannan wata na Janairu ake sa ran cewa, majalisar zartarwar FIFA zata cinmma matsaya game da bukatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.