Isa ga babban shafi
Wasanni

Ronaldo yayi fice a shafukan sadarwar zamani

Gwarzon dan wasan kwallon kafa na Duniya da ya lashe kyautar Ballond’Or ta shekarar 2016, Cristiano Ronaldo, ya samu nasarar zama dan wasan kwallon kafa da ya fi kowanne mamaye kafafen sardarwar zamani a wannan shekara.

Cristiano Ronaldo
Cristiano Ronaldo Reuters / Kim Kyung-Hoon
Talla

Wani rahoton da wata cibiyar bincike kan batutuwan da ke gudana a kafafen sadarwar Internet mai suna CrowdTangle ta gudanar, ya nuna cewa Ronaldo ke kan gaba tsakanin takwarorinsa wajen mamaye shafukan dandanlin Facebook.

Zalika cibiyar ta CrowdTangle ta ce sama da mutane miliyan 34 ne ke nuna goyon bayansu ga dukkanin bayanan bajintar da Ronaldo da aka wallafa a shafukan na internet.

A wata zantawa da yayi da manema labarai, Ronaldo ya bayyana shekara ta 2016, a matsayin shekarar da bazai manta da ita ba a tarihin rayuwarsa, saboda nasarorin da ya samu.

Ronaldo ya taimakawa kasarsa ta Portugal lashe kofin gasar nahiyar Turai, sai kuma lashe kofin gasar zakarun kungiyoyin kwallon kafa na nahiyar turai tare da kungiyarsa ta Real Madrid.
A wannan shekara ce kuma Ronaldo ya lashe kyautar Ballond’Or, ta gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya karo ma 4.

Zalika a wannan shekara Cristiano ya taimakawa kungiyarsa ta Real Madrid lashe kofin gasar zakarun kungiyoyin kwallon kafa na Duniya da aka kammala ta a kasar Japan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.