Isa ga babban shafi
Wasanni

FIFA ta sassauta wa Real Madrid hukunci

Hukumar kwallon kafa ta duniya ta sassauta hukuncin da ta dauka kan Real Madrid na haramta mata cefanan ‘yan wasan har na tsawon kakannin wasanni biyu.

'Yan wasan Real Madrid
'Yan wasan Real Madrid
Talla

Wannan ya biyo bayan karar da Real Madrid ta daukaka ne a kotun sasanta rikcin wasanni don kalubalntar hukuncin na FIFA.

Yanzu haka dai, Real Madrid ba ta da hurumin siyan ‘yan wasa a cikin watan Janairu mai zuwa amma an amince ta yi cefanan su  a kakar wasanni ta gaba.

Kazalika an rage tarar da FIFA ta ci Real Madrid daga Pam dubu 282 zuwa Pam dubu 188.
 

An dai hukunta Real Madrid ne bayan ta siyi 'yan wasa masu kasa da shekaru 18 daga kasashen waje, abin da ya saba da dokar FIFA.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.