Isa ga babban shafi

Barcelona za ta dauki matakin shari'a kan kwallonta da VAR ta soke a El Clasico

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Joan Laporta ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen daukar matakin shari’a don bin diddigin hakikanin sahihancin kwallon da alkalin wasa ya hana kungiyar yayin wasan El Classico tsakaninsu da Real Madrid a karshen mako.

Mai horas da kungiyar Kwallon kafa ta Barcelona
Mai horas da kungiyar Kwallon kafa ta Barcelona REUTERS - Sarah Meyssonnier
Talla

Matashin dan wasa Lamine Yamal ne ya zura kwallon amma kuma alkalin wasa da na’urar VAR suka ki amincewa da shigarta raga, lamarin da ya haddasa cece-kuce hatta a tsakanin bangarorin masana.

An dai tashi wasa tsakanin Barcelonar da Real Madrid 2 da 3, maimakon 3 da 3 da Barcelonar ke ganin haka yakamata sakamakon ya kasance.

Barcelona dai ta yi amannar cewa kwallon ta Yamal ta tsallaka layin raga gabanin Andriy Lunin ya hankadota waje.

A cewar Laporta, Barcelona za ta bukaci samun damar isa ga faifan bidiyo da kuma sautin da aka nada na musayar bayanan mambobin kwamitin kwararrun alkalan wasan na ranar Lahadi daga hukumar kwallon kafar Spain don bibiya tare da tabbatar da sahihancin kwallon ko akasin haka.

Shugaban na Barcelona ya bayyana cewa suna da kwarin gwiwar yiwuwar samun matsala a a musayar bayanan da ta soke ko kuma kin amincewa da kwallon ta Yamal.

Joan Laporta ya ce Barcelona za ta dauki duk matakan da suka dace na shari’a don ganin ta bi kadin kwallon na ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.