Isa ga babban shafi

Dole sai magoya bayan Manchester United sun yi hakuri - Ratcliffe

Guda cikin mamallaka kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Sir Jim Ratcliffe ya bayyana cewa, dole magoya bayan kungiyar su yi hakuri da tsare-tsarensa bayan kasancewarsa guda cikin mafiya rinjayen hannun jari a kungiyar.

Sir Jim Ratcliffe guda cikin masu rike da mafi rinjayen hannun jarin kungiyar kwallon kafa ta Manchester United.
Sir Jim Ratcliffe guda cikin masu rike da mafi rinjayen hannun jarin kungiyar kwallon kafa ta Manchester United. © AFP / VALERY HACHE
Talla

Cikin watan Fabarairu ne Ratcliffe ya kulla yarjejeniyar sayen kashi 27.7 na hannun jarin Manchester United kan yuro biliyan 1 da miliyan 250 kuma tun daga wancan lokaci ya ke gabatar da gyare-gyaren da ya ce su ne za su daga darajar kungiyar don dawo da kimarta.

A cewar Ratcliffe mai shekaru 71 tafiya ta fara nisa a gyare-gyaren da ya ke a United, kungiyar da yanzu haka ke matsayin ta 7 a teburin firimiyar Ingila ko da ya ke ta samu tikitin wasan karshe na cin kofin FA bayan doke Coventry da kyar.

Amma duk da wannan nasara ta United akwai jan aiki a gabanta, lura da yadda ta ke shirin haduwa da takwararta Manchester City a wasan karshe na gasar ta cin kofin FA, kuma masu sharhi na ganin abu ne mai matukar wuya tawagar ta Red Devils ta iya kai labari a hannun yaran na Pep Guardiola wadanda damar lashe kofin zakarun Turai ta kufce musu bayan shan kaye a hannun Real Madrid ta Spain.

Sai dai Ratcliffe ya ce sabbin gyare-gyare na tafe zuwa karshen kaka kuma dole sai magoya baya sun yi hakuri, batun da ke kara tabbatar da jita-jitar yiwuwar kungiyar yin juye ciki har da mai horarwa Erik ten Hag.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.