Isa ga babban shafi

Liverpool ta sha kaye a hannun Everton karon farko cikin shekaru 14

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta sha kaye a hannun Everton da kwallaye 2 da nema yayin karawarsu ta daren jiya Laraba da ta kawo karshen fatan Reds na lashe kofin firimiyar Ingila a bana.

Wata haduwar Liverpool da Everton.
Wata haduwar Liverpool da Everton. POOL/AFP
Talla

Nasarar ta Everton kan Liverpool a filin was ana Goodison Park ita ke matsayin karon farko da kungiyar ta yi tun bayan makamanciyarta a watan Oktoban shekarar 2010, nasarar da kuma ta wargaza fatan Reds a tseren da ta ken a lashe kofin gasar ta Firimiya.

Tun a zagayen farko ne Everton ta zura kwallo guda gabanin kara kwallo ta 2 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, a wani yanayi da ba a yi zato ba, wanda ya sanya daukacin filin wasan na Goodison Park kaurewa da kuwwa.

Mai tsaron ragar Everton Jordan Pickford yan una matukar bajinta bayan tare jerin kwallayen da ‘yan wasan Liverpool suka rika yunkurin zurawa, yayinda takwaransa Alisson Becker ya yi kuskuren da ya kai ga shan kwallaye har guda biyu.

Magoya bayan Everton sun rika rera wake mai taken “Kun rasa kofin firimiya a Goodison Park” waken da ke da nufin fusata tawagar ta Jurgen Klopp wadanda kofin ya kufcewa kai tsaye daga wannan wasa.

Shekaru 39 kenan cif rabon da Everton ta yi gagarumar nasara irin wannan a filin wasan na ta na Goodison Park lokacin da ta doke Bayern Munich a wasan gab da na karshe na cin kofin Turai.

Daren na jiya dai zai kasance mai matukar tarihi da magoya bayan Everton za su shafe shekaru suna tunawa da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.