Gasar Firimiya: Arsenal da Liverpool sun ɓarin da ba lallai su kwashe daidai ba
Kungiyoyin Arsenal da Liverpool sun yi ɓarin makin da ya bai wa abokiyar hamayyarsu Manchester City damar ɗarewa saman teburin gasar Firimiyar Ingila.
Wallafawa ranar:
Liverpool ce dai ta fara shan kaye da kwallo 1-0 yayin karawar da tayi da Crystal Palace a ranar Lahadi.
Mintuna bayan wasan na Liverpool ne kuma Arsenal ma ta karɓi nata kason kwallayen har guda biyu ba tare da rama ko da guda ba, abinda ya sa Aston Villa lallasa ta da 2-0.
A halin yanzu Manchester City na kan gaba a gasar Firimiyar Ingila ta maki 73, yayin da Arsenal ke matsayin ta biyu da maki 71, Liverpool ta uku itama da maki 71, sai dai yawan kwallayenta bai kai na ‘Gunners’ ba.
Wasanni 6 kawai suka rage a ƙarƙare gasar Firimiyar bana, abinda ya sa ƙungiyar City kama hanyar sake lashe kofin gasar karo na huɗu a jere.
Tun a ranar Asabar da ta gabata, kungiyar ta dare saman teburin Firimiya bayan wasan da ta lallasa kungiyar Luton da 5-0.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu