Liverpool ta haye teburin gasar Firimiyar Ingila
Manchester City da Arsenal sun ɗaga darajar Liverpool a gasar Premier sakamakon canjaras da suka yi babu ci a wasan da suka buga a Etihad.
Wallafawa ranar:
A yanzu Liverpool ce ta daya a saman teburi da maki biyu tsakaninta da Arsenal da City kuma maki uku, bayan da ta doke Brighton a filin wasa na Anfield, saboda abokan hamayyar su biyu sun raba maki ɗaya-ɗaya.
Ƙwallon Mohammed Salah ne ya taimakawa Liverpool doke Brighton da ci 2 -1 a wasan da suka fafata ranar Lahadi a Anfield.
Kocin Arsenal Mikel Arteta zai yi farin ciki fiye da takwaransa na City Pep Guardiola da wannan sakamakon – amma kuma Jurgen Klopp na Liverpool zai fi su jin daɗi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu