Isa ga babban shafi

Liverpool da Manchester City sun yi canjaras a gasar Firimiya 1-1

Liverpool da Manchester City sun tashi kunnen doki 1-1 a karawar da suka yi a gasar cin kofin Firimiya da suka bar Arsenal a saman teburin, yayin da Tottenham ta lallasa Aston Villa da ci 4-0, abin da ya sake farfado da yunkurinsu na zuwa gasar ta hudu a ranar Lahadi.

Wasu daga cikin magoya bayan kungiyar Manchester City
Wasu daga cikin magoya bayan kungiyar Manchester City REUTERS - KEMAL ASLAN
Talla

Manchester City ce ta fara cin kwallo ta hannun John Stones a farkon wasan, amma Alexis Mac Allister ya rama kwallon da bugun fenareti jim kadan bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a Anfield.

Erling Haaland dan wasan Manchester City
Erling Haaland dan wasan Manchester City AFP - PAUL ELLIS

Sakamakon ya kasance daidai abin da Arsenal ke so yayin da Gunners ta ci gaba da zama a matsayi na farko, matsayin da ta samu lokacin da Kai Havertz ya ci da kai a karshen wasan da suka doke Brentford da ci 2-1 a ranar Asabar.

Yan wasan Manchester City
Yan wasan Manchester City AP - Manu Fernandez

Arsenal ce ta sama da Liverpool ta biyu da maki 7, yayin da City mai rike da kambun ta ke tazarar maki daya tsakaninta da ta biyu, inda dukkanin kungiyoyin uku ke da sauran wasanni 10.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.