Isa ga babban shafi

Unai Emery ya tsawaita yarjejeniyar horar da Aston Villa zuwa 2027

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Aston Villa Unai Emery ya tsawaita yarjejeniyar zamansa a kungiyar har zuwa nan da shekarar 2027, dai dai lokacin da kungiyar tasa ke matsayin ta 4 a teburin firimiyar Ingila.

Unai Emery, mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Aston Villa.
Unai Emery, mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Aston Villa. AFP/Archivos
Talla

Emery wanda ya karbi kungiyar daga hannun Steven Gerrard a watan Nuwamban 2022 lokacin ta na matsayin ta 17 a teburin firimiya ta na kokarin tsallake rukunin ‘yan dagaaji.

Villa dai ta yaba da yadda Emery dan Spain mai shekaru 52 ya sauya zubin wasan kungiyar cikin kankanin lokacin da ya dauka ya na jagoranci wanda ya basu damar haskawa a gasar Europa Conference League cikin kakar da ta gabata, gasar da rabon Aston Villa ta haska a cikinta tun kakar wasa ta 2010 zuwa 2011.

A yanzu da kungiyar ke matsayin ta 4, idan har ta kammala wasannin firimiyar wannan kaka ba tare da matsar da ita daga gurbin da ta ke ba, kenan kai tsaye za ta haska a gasar cin kofin zakarun Turai karon farko bayan daukar tsawon lokaci.

Ana dai kallon wannan kokari a matsayin dalilin da ya bai wa kungiyar karin gwiwar bawa Emery damar tsawaita yarjejeniyar aikin nasa zuwa nan da shekarar 2027.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.