Isa ga babban shafi

Da yiwuwar Arne Slot ya karbi ragamar horar da Liverpool daga Klopp

Wasu bayanai na nuna cewa mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Fayenoord da ke Holland Arne Slot na matsayin ‘yan gaba-gaba a jerin manajojin da ke rige-rigen maye gurbin Jurgen Klopp a Liverpool, bayan da manajan ke shirin ajje aiki a karshen wannan kaka.

Feyenoord coach Arne Slot
Feyenoord coach Arne Slot © REUTERS/Kacper Pempel
Talla

A watan Janairun da ya gabata ne Klopp ya sanar da shirin barin Anfield a karshen wannan kaka, kuma tun daga wancan lokaci kungiyar ke laluben wanda zai maye gurbinsa.

Sai dai bayanan baya-bayan nan sun ce Slot ne ya cika dukkanin sharuddan da Liverpool ta gindaya na manajan da za ta dauka don maye gurbin.

Slot mai shekaru 45 da ya jagoranci Feyernoord wajen lashe kofin Eredivisie a kakar da ta gabata, baya ga lashe kofin Dutch a wannan kaka, dai dai lokacin da kungiyar da ya ke jagoranta ke matsayin ta 2 a teburin babbar gasar ta Eredivisie.

Ko a bara Slot da kansa ya ki amincewa da karbar aikin horarwar da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham wadda ta yi masa tayin aiki a wancan lokaci.

Haka zalika ko kungiyoyin kwallon kafa na Bayern Munich da Barcelona sun yi harin mai horarwa amma yaki amincewa da karbar aikin ko da ya ke ya nuna sha’awar karbar ragamar Reds a wannan karon.

Baya ga Slot masu horarwa irinsu Xabi Aonso na Bayer Leverkusen da manajan Sporting Lisbon wato Ruben Amorim na sahun wadanda ake alakantawa da karbar aikin horar da tawagar ta Liverpool a karshen kaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.