Isa ga babban shafi
Wasanni

Mourinho na da damar lashe gasar FA

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya kara farfado da damarsa ta lashe kofin gasar FA a wannan kakar bayan kungiyarsa ta doke Hull City da ci 2-0 a wasan da suka yi a zagaye na farko a matakin wasan dab da na karshe. 

Kocin Manchester United, José Mourinho.
Kocin Manchester United, José Mourinho. REUTERS/John Sibley/File
Talla

Hankula sun karkara ne akan keften din kungiyar Wayne Rooney da ke neman ci wa Manchester United kwallo ta 250 a wasan na jiya amma hakan ya ci tura, in da Juan Mata ya fara jefa kwallon farko a minti na 56 kafin daga bisani Marouane Fellaini ya jefa ta biyu a minti na 87.

A ranar 26 ga wannan watan na Janairu ne kungiyoyin biyu za su sake haduwa fafatawa a zagaye na biyu.

A karo na tara kenan da Manchester United ke samun nasara a jere a wasannin da ta yi na baya-bayan nan, kuma a ranar Lahadi mai zuwa ne za ta fafata da Liverpool a gasar Premier ta Ingila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.