Isa ga babban shafi
Wasanni

An gano wasika a inda aka kai wa kungiyar Borussia Dortmund hari

‘Yan sanda a kasar Jamus suna cigaba da gudanar da bincike kan harin da aka kai kan motar ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund da abubuwan fashewa.

Motar 'yan wasan kungiyar Borussia Dortmund bayan harin abubuwan fashewa da ake zargin an nufi kai wa kan 'yan wasan.
Motar 'yan wasan kungiyar Borussia Dortmund bayan harin abubuwan fashewa da ake zargin an nufi kai wa kan 'yan wasan. Reuters
Talla

Abubuwan fashewar har guda 3 sun tarwatse ne yayinda ‘yan wasan na Dortmund ke kan hanyar isa Filin wasansu na Iduna don karbar bakuncin kungiyar Monaco daga Faransa lamarin da yayi sanadin raunata dan wasansu Marc Bartra.

Shugaban ‘yan sandan garin Dortmund, Gregor Lange, ya ce sun samu wata wasika a dai dai inda harin ya auku, sai dai yaki bayyana abinda takardar ta kunsa, inda ya ce sai sun tantance sahihancin wasikar kafin gabatar da karin bayani.

Babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, wanda har yanzu ‘yan sandan Jamus basu kai ga gano dalilin kai shi ba.
Kafin kai harin ‘yan sanda sun tabbatar da cewa babu wata barazanar tsaro a yankin da filin wasan na kungiyar Dortmund wato Iduna, wanda ke daukar ‘yan kallo 80,000, mafi girma a kasar Jamus.

A yau ne za’a buga wasan tsakanin Borussia Dortmund da Monaco abayan dage wasan da aka yi a jiya.

Zalika a sauran wasannin gasar cin kofin zakarun nahiyar turai kuma, za’a fafata tsakanin Real Madrid da Bayern Munich sai kuma Leicester City da Atletico Madrid.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.