Isa ga babban shafi
Wasanni

Toure ya ce karawarsu da Man Utd zai fi son a ce babu alkalin wasa

Dan wasan Manchester City Yaya Toure ya ce haduwarsu da Manchester United a gasar Frimiya ingila ranar Alhamis zai fi son a ce babu alkalin wasa.

Yaya Touré na Manchester City
Yaya Touré na Manchester City Reuters / Phil Noble
Talla

Toure ya fadi hakan ne yayin sokar yadda aka gudanar da alkalanci fafatawar da Arsenal ta hanasu zuwa wasan karshe na cin kofin FA.

Alkalin wasa Craig Pawson ya hana kwallon da Sergio Aguero ya ci, kan dalilin cewa kwallon ta yi waje tun da farko kafin Aguero ya same ta.

Batun da Toure ya ce wannan ba shi ne karon na farko da suke samun irin haka a wasa ba.

Toure ya ce, abin ya ba shi takaici, yana ganin ya kamata alkalan wasa su daina haka, kuma suna fatan a samu alkalin da ya fi Pawson ko kuma ayi wasan babu alkalin, don shi yafi son haka.

Fafatawar Man City da Utd na da muhimmaci tsakanin kungiyoyin na hamayya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.