Isa ga babban shafi
Wasanni

Ronaldo ya sake kafa tarihi da kwallaye 103 a Zakarun Turai

Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ya sake kafa tarihi bayan zura kwallaye 3 a ragar Atletico da yammacin jiya talata.

Dan wasan tsakkiyar fagen kungiyar Real Madrid Cristiano Ronaldo
Dan wasan tsakkiyar fagen kungiyar Real Madrid Cristiano Ronaldo REUTERS/Sergio PerezREUTERS/Sergio Perez
Talla

Wasan da suka fafata zagaye farko ya kasance kusa karo na 3 cikin jeren shekaru 4 da Real Madrid ke doke Makawabciyarta Atletico.

Atletico Madrid ta kai hari guda daya tilo wanda tsautsayi ya hana kwallon shiga raga.

Yanzu dai Ronaldo yazura kwallaye 103, adadin mafi yawa da dan wasa ke zurawa a tarihin wasanni cin kofin zakarun Turai.

Kuma wannan ne karo na 13 da dan wasan ya ke zuwa wasan kusa da na karshe na gasar ta zakarun Turai.

Shekaru 4 a jere da kungiyoyin ke haduwa, Real Madrid ce ke doke Alteletico a shekarar 2014 da 2016 da kuma wasan gab da na karshe a 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.