Isa ga babban shafi
Europa

Manchester United da Ajax za su hadu a wasan karshe a Europa

Manchester United da Ajax ne za su hadu a wasan karshe a gasar Europa lig bayan sun fitar da Celta Vigo da Lyon a zagayen kusa da karshe da suka fafata.

Manchester United ta kai zagayen karshe a gasar Europa Lig bayan ta fitar da Celta Vigo
Manchester United ta kai zagayen karshe a gasar Europa Lig bayan ta fitar da Celta Vigo REUTERS
Talla

Manchester ta tsallake da jimillar kwallaye 2-1 akan Celta Vigo, bayan sun yi kunnen doki ci 1-1 a Old Trafford. Manchester ta samu nasara cin Celta Vigo ci 1-0 a karawa ta farko da suka yi a Spain.

Ajax ta tsallake ne da jimillar kwallaye 5-4, duk da Lyon ta doke ta 3-1 a fafatawar da suka yi a jiya.

A karawa ta farko Ajax ta doke Lyon ne ci 4-1.

Baya ga lashe kofin Europa, kuma dama ce ga Manchester United da Ajax na samun hurumin shiga gassar zakarun Turai.

Tuni Mourinho kocin Manchester ya bayyana cewa hankalin shi ya dawo ga kokarin lashe Europa domin samun shiga gasar zakarun Turai a kaka mai zuwa.

Yana da wahala Manchester ta samu shiga gasar ta hanyar gasar premier bayan ta sha kashi a hannun Arsenal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.