Roland Garros: Nadal zai hadu da Wawrinka a wasan karshe
Rafael Nadal ya tsallake zuwa zagayen karshe a gasar Tennis ta Roland Garros da ake gudanarwa a Faransa bayan ya doke dan wasan Australia Dominic Theim ci 6-3, 6-4, 6-0 a yau Juma’a.
Wallafawa ranar:
Karo na 10 ke nan da Nadal na kai zagayen karshe a yayin da yak e harin lashe kofin gasar karo na 10.
A shekarar 2014 ne Nadal ya lashe kofin gasar karo na 9.
Yanzu Rafael Nadal zai hadu da Stan Wawrinka a wasan karshe wanda ya doke Andy Murray na Birtaniya.
Wawrinka mai shekaru 32 ya kasance dan wasa mai yawan shekaru da ya kai zagayen karshe a Roland Garros tun shekarar 1973.
A bangaren Mata ‘yar kasar Latvia Jelena Ostepenko ce ta lashe kofin gasar bayan ta doke Simona Halep ta Romania a wasan karshe da suka fafata a yau Juma’a.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu