Isa ga babban shafi
Wasanni

Ronaldo ya musanta kauce wa biyan haraji

Gwarzon dan wasan duniya kuma dan asalin kasar Portugal Christiano Ronaldo ya musanta zargin kauce wa biyan haraji bayan masu gabatar da kara a Spain sun ce ya ki biyan hukumomin kasar harajin Euro miliyan 14.7 tsakanin shekarar 2011 zuwa 2014.

Cristiano Ronaldo na Real Madrid
Cristiano Ronaldo na Real Madrid © Reuters / Michael Dalder Livepic
Talla

Ofishin masu gabatar da karar da ke birnin Madrid ya ce, tuni ya shigar da karar Ronaldo a kotu don fuskantar hukunci.

Sai dai wata sanarwa da wakilan Ronaldo suka fitar ta ce, dan wasan na Real Madrid bai yi wata rufa-rufa ba don kauce wa wajen biyan harajinsa.

Sanarwar ta ce, bai boye wa hukumomin Spain abin da ya ke samu na kudi ba.

Dan wasan shi ne ya fi dukkanin wani dan wasa a duniya karbar albashi a yanzu, kamar yadda mujallar Forbes ta ambata.

A bara kadai, Ronaldo ya karbi albashin Dala miliyan 93 da suka hada da alawus-alawus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.