Wasanni
Najeriya zata karbi bakuncin gasar kokowa ta nahiyar Africa
Najeriya ta samu nasarar zama kasar da zata karbi bakuncin gasar kokokowa ta nahiyar Africa, wadda zata gudana daga ranar 7 zuwa 11 ga watan Fabarairun shekara ta 2018, bayan da ta kada kasar Tunisia da itama ta nemi wannan dama.
Wallafawa ranar:
Talla
Kasashen 43 ne ake sa ran zasu fafata a gasar ta kokokowa, wadda karo na farko kenan Najeriya zata karbi bakuncinta, tun bayan shekarar 1976.
Tuni dai gwamnatin Jihar Rivers da ke kudancin kasar ta bayyana cewa a shirye ta ke ta karbi wannan nauyi, na gudanar da gasar a cikinta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu