Barcelona ta cimma matsaya da Dortmund a kan Dembele
Kungiyar Barcelona ta cimma matsaya da takwararta ta Borussia Dortmund domin sayan dan wasanta Ousmane Dembele kan kudi fam miliyan 97.
Wallafawa ranar:
Dembele mai shekaru 20, wanda kuma da wasan gaba ne na tawagar kwallon kafar kasar Faransa, zai isa Barcelona ne a ranar Lahadi, yayinda kuma za’a gwada lafiyarsa a ranar Litinin, kafin daga bisani ya sanya hannu kan yarjejeniyar bugawa kungiyar wasanni, tsawon shekaru biyar.
Kungiyar Barcelona ta warewa Dembele riga mai dauke da lamba 11.
Dembele shi ne dan wasan gaba na farko da Barcelona ta saya, tun bayan tafiyar Neymar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu