Isa ga babban shafi
Wasanni-Ingila

Wasan da Liverpool at lallasa Arsenal 4-0 ya bar baya da kura

Bisa Dukkanin alamu lallasa Arsenal da kungiyar Liverpool ta yi a wasan da suka buga ranar Lahadin da ta gabata ya bar baya da kura, domin kuwa watanni uku bayan sabunta yarjejeniyar cigaba da horar da Arsenal, Wenger har ma da ‘yan wasan na fuskantar suka da Ala Wadai.

Mai horar da kungiyar Arsenal, Arsene Wenger, lokacin wasan da Liverpool ta lallasa su da kwallaye 4-0.
Mai horar da kungiyar Arsenal, Arsene Wenger, lokacin wasan da Liverpool ta lallasa su da kwallaye 4-0. Reuters/Carl Recine
Talla

Domin kuwa yayinda tsaffin ‘yan wasan kkungiyar kamar su Thiery Henry, ya hada ‘yan wasan da mai horarwar yayi musu kudin goro, wajen zarginsu da gaza tabukawa kungiyar komai, shi kuwa tsohon dan wasa Ian Wright, da ya ci wa Arsenal kwallaye 128, cewa yayi ya kamata Wenger ya tattara ya kara gaba an gode hakanan.

A cewar Wright dukkan alamu sun gama tabbata cewa Wenger ba zai iya sake yin wani tasiri ba wajen sanya karsashi ko karawa ‘yan wasansa kwarin gwiwa.

A watan Mayun da ya gabata Wenger ya sanya hannu kan cigaba da horarwa tsawon shekaru 2, duk da kiraye kirayen a sallame shi, sakamakon gaza halartar gasar zakarun turai, wanda Arsenal bata taba fashi ba tun cikin shekaru 20.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.