Sai an maimaita wasan Afrika ta kudu da Senegal- FIFA
Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta bukaci a maimaita wasan neman shiga gasar cin kofin duniya da aka fafata tsakanin Afrika ta kudu da Senegal bayan samun alkalin wasan da yin coge.
Wallafawa ranar:
FIFA ta dakatar da Alkalin wasan dan Ghana Joseph Lamptey har abada bayan ya yi coge a alkalancin wasan da Afrika ta kudu da Senegal suka buga a watan Nuwamban 2016.
Afrika ta kudu ce ta yi nasara da ci 2-1 bayan alkalin ya ba kasar wani fanariti da har ya janyo aka dakatar da shi.
Matakin maimata wasan dai yanzu na zuwa a yayin da Senegal ke matsayi na uku a rukuninsu na D a yayin da kuma ya rage wasanni biyu.
A watan Nuwamba mai zuwa kasashen biyu za su sake fafatawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu