Isa ga babban shafi
Wasanni

Ghana ta lashe kofin gasar WAFU

Tawagar kwallon kafa ta kasar Ghana ta lashe kofin gasar kwallon kafa ta kasashen yammacin Afrika WAFU, bayan lallasa Super Eagles ta Najeriya da kwallaye 4-1, a wasan karshe da suka fafata jiya Lahadi.

Tawagar kwallon kafa ta kasar Ghana.
Tawagar kwallon kafa ta kasar Ghana. REUTERS/Toussaint Kluiters/United Photos/Files
Talla

Bayan nasarar lashe kofin, tawagar kwallon kafar kasar ta Ghana ta samu kyautar Dala Dubu 100.

Yayin gudanar da gasar a matakin rukuni, Najeriya ta lallasa tawagar kasar ta Ghana da kwallaye 2-0.

Yayin da Najeriya ke a matsayi na biyu a gasar cin kofin na WAFU, Jamhuriyar Nijar ce ta lashe lambar tagulla, bayan da ta lallasa Jamhuriyar Benin da kwallaye 2-1, ta kammala gasar kenan a matsayi na uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.