Isa ga babban shafi
Wasanni

An dakatar da shugaban kungiyar Juventus tsawon shekara 1

Hukumar kwallon kafa ta kasar Italiya ta dakatar da shugaban kungiyar Juventus Andrea Agnelli daga aiki tsawon shekara guda, sakamakon samunsa da laifin saida tikitin shiga kallon wasannin kungiyar ba bisa ka’ida ba, ga wasu kungiyoyin magoya bayan kungiyar ta Juventus da basu cancanta ba.

Shugaban kungiyar Juventus Andrea Agnelli.
Shugaban kungiyar Juventus Andrea Agnelli. REUTERS/Giorgio Benvenuti
Talla

Sakamakon laifin, Agnelli zai kuma biya tarar euro 20,000, yayinda ita kuma kungiyar ta Juventus zata biya tarar euro 300,000, sai kuma wasu manyan jami’anta uku da suma aka dakatar saboda hannunsu cikin saida tikitin.

Da fari dai mai gabatar da kara Giuseppe Pecoraro, ya bukaci a haramtawa shugaban kingiyar ta Juventus Agnelli, shiga al’amuran wasannin ne tsawon shekaru 2 da rabi, ya kuma biya tarar euro dubu hamsin, a maimakon euro dubu ashirin da hukumar kwallon kafar ta ce ya biya a yanzu.

Sai dai fa Pecoraro ya ce yana tunanin komawa wata kotun ta daban banda ta hukumar wasannin, domin kara tsaurar hukuncin kan kungiyar ta Juventus da mai horar da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.