Isa ga babban shafi
wasanni

Iceland ta samu gurbi a gasar kofin duniya a karon farko

A karon farko a tarihi, tawagar kwallon kafa ta Iceland ta samu gurbi a gasar cin kofin duniya da za a gudanar a Rasha bayan ta casa Kosovo da ci 2-0 a fafatawar da suka yi a jiya Litinin.

Tawagar kwallon kafa ta Iceland ta kafa tarihin zuwa gasar cin kofin duniya a karon farko
Tawagar kwallon kafa ta Iceland ta kafa tarihin zuwa gasar cin kofin duniya a karon farko Reuters
Talla

Wannan gagarumar nasarar na zuwa ne bayan watanni 18 da Iceland ta fitar da Ingila a zagaye na biyu a gasar cin kofin kasashen nahiyar Turai.

Iceland ita kadai ce kasa a duniya mai yawan al’umma kasa da miliyan 1 da ta samu gurbi a gasar cin kofin duniya.

Kocin tawagar kasar Heimir Hallgrimsson ya ce, nasarar da suka samu ba ita ce karshe ba, domin kuwa akwai sauran gacin da suke fatan kai wa nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.